Majalisar Matasa a Najeriya da kuma gwamnatin Jihar Taraba suka shirya wannan taron domin a samu hanyoyin samarwa da matasa sana'o'in da zasu kawar da hankulansu daga shiga ayyukan rashin da'a da koyan zaman tare da juna cikin lumana.
A wajen wannan taron, kwararru da shugabanni da sauran jama'a duk sun yi jawabai kan muhimmancin zaman tare. Shugabannin matasa a Taraba sun ce zasu yi kokarin tabbatar da cewa 'yan'uwansu matasa ba su zamo karnukan farautar 'yan siyasar dake neman cimma gurinsu ta hanyar amfani da matasan domin aikata laifi ba.
Suka ce muhimmin abu shi ne tabbatar da cewa matasa sun yi zaman tare da junansu ba tare da bambancin addini ko kabila ko bangare ba.
Shugabanni a jihar, cikinsu har da mukaddashin gwamna Garba Umar, yace sun debi matasa masu yawan gaske domin samar musu da ayyukan yi da nufin kaucewa yiwuwar fadawarsu cikin ayyukan bangar siyasa.
Ibrahim Abdulaziz ya aiko da cikakken bayani kan wannan taron.