Duka duka, alkaluman da kamfanin dillancin labaran Associated Press ya tattara na tsawon watanni 9, daga ranar 5 ga watan Oktoban 2012 zuwa ranar 5 ga watan Yulin 2013, sun nuna cewa sojojin gwamnatin Najeriya sun kashe dubban mutane a yunkurinsu na kashe wutar kayar bayar ‘yan Boko Haram.
Wadannan alkaluma na wadanda aka kashe din ma an samo su ne daga asibiti kwaya daya tak a Maiduguri, watau asibitin Koyarwa na Kwararru na Sani Abacha dake wannan gari, inda nan ne cibiyar kungiyar ta Boko Haram.
A cikin kwanaki 30 da suka zo kafin a ayyana dokar-ta-baci a ranar 14 ga watan Mayu, sojoji sun kai gawarwakin mutane 380 zuwa asibitin. A cikin kwanaki 30 bayan ayyana dokar-ta-bacin kuwa sojoji sun kai gawarwaki 1,321 (dubu daya da dari uku da ashirin da daya).
A cikin watan Yuni, yawan gawarwakin da sojoji suka kai wannan asibiti kwaya daya tak, sun kai 1,795 (dubu daya da dari bakwai da casa’in da biyar), a bisa alkaluman da kamfanin dillancin labaran na AP ya yi nazarinsu, inda jami’an kamfani n da idanunsu suka ga motocin soja tare da rakiyar motoci masu sulke, su na kai gawarwaki cikin asibitin.
Wannan adadin ya zarce yawan mayakan da aka kiyasta cewa kungiyar Boko Haram tana da su.
Jami’an gwamnati da na rundunar sojojin Najeriya sun ki yarda su ce komai a kan wannan batun, kuma yana da wuya a san ko nawa ne daga cikin wadannan matattu suke da wata alaka da kungiyar Boko Haram. Amma dokokin Najeriya sun yi tanadin cewa koda a karkashin dokar-ta-baci ma, tilas ne a kai duk wani mutumin da aka kama gaban alkali cikin sa’o’I 48, a kuma kyale shi ya ga lauya ko iyalansa.
A wannan makon, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce daruruwan fursunoni su na mutuwa a hannun sojoji a wuraren da aka kama su. Ta ce wasu ana fito da su daga dakunan da aka kulle su ana harbe su, wasu su na mutuwa saboda yunwa, yayin da wasu ke mutuwa saboda tsananin cunkoso.
Kungiyar kare hakkin Adamar ta ce wani bayani mai tushe da ta samu daga wani babban hafsan sojan Najeriya ya nuna cewa an kashe mutane fiye da 950 haka siddan a watanni 6 na farkon wannan shekara.
Alkaluman da kamfanin dillancin labaran AP ya gani a asibiti kwaya daya tak a Maiduguri cikin wannan lokacin, sun nuna cewa gawarwaki 3,335 (dubu uku da dari uku da talatin da biyar) aka kai wannan asibitin cikin wadannan watanni shidan da ake magana.