A lokacin da ta kai ziyarar gaisuwar Sallah ga alhazan na Jihar Neja a masaukinsu a birnin Makkah, Hajiya Jummai Babangida Aliyu, ta taya alhazan murnar kammala aikin Hajji cikin nasara tare da fatan Allah Ya karbi ibadarsu.
Amirul Hajj na Jihar Neja, kuma mataimakin gwamnan Jihar, Alhaji Ahmed Musa Ibeto, ya bayyana cewa sun dauki matakai da dama a bana na tabbatar da cewa alhazan jihar ba su gamu da wata matsala a lokacin aikin hajjin ba, kuma sun samu nasarar hakan.
Jami'an sun kai wannan ziyara a daidai lokacin da alhazan jihar ta Neja suke jimamin rasuwar wani mahajjaci guda daga karamar hukumar Chanchaga wanda ya rasu a Makka. Hukumomin Sa'udiyya dai su na binciken musabbabin rasuwarsa.
Ga cikakken rahoton da Mustapha Nasiru Batsari ya aiko daga Makka.