Wakilin sashin Hausa Ibrahim Alfa Ahmad a wata hirarsu da Ibrahim Ka’almasih Garba, ya ruwaito cewar yayinda Farfesa Attahiru Jega ya mika ma Janar Muhammadu Buhari takardar shaidar lashe zaben na 2015, shugaban ya gabatar da jawabin da ya sosa zuciyar jama’a.
A cikin jawabin sa, shugaban yace duk da yanayin mulkin jam’iyar PDP da tasha kaye a wannan zaben gashi ga yadda yake, a matsayinsa na sabon shugaba yana mika masu hannu domin suyi aiki tare.
Sabon shugaban yayi Magana akan batutuwa da dama kamar su cin hanci da rashawa da batun yaki da boko haram inda yace, zai bada kokari wajan wanzar da zaman lafiya da kuma kawo karshen ta’addancin dake faruwa a wasu sassan kasar.
Ya kuma kara da cewa yanzu ne ‘yan ta’adda zasu san cewa ra’ayi da akida da karfin ‘yan Najeriya ya hadu wuri daya ta wajan yakar su. Kuma duk abinda Najeriya ta mallaka zatayi amfani dashi domin cimma wannan buri.
Jama’a da dama sun rasa rayukansu wajan bukukuwan farin ciin samun wannan nasarar lashe zaben da Janar Muhammadu Buhari yayi, dan haka yasa akayi shiru na wani dan lokaci domin karramawa tare da yin addu’a ma wadanda suka rasa rayukan su akan wannan al’amari.