Janar Muhammad Buhari ya yi juyayin ne lokacin da ake mika masa takardar cewa ya lashe zaben shugaban kasa.
Yace abun juyayi ne matuka a ce wadansu sun rasa rayukansu wasu kuma da dama sun samu raunuka saboda murnar nasarar da ya samu. Akan haka ne ya yi kira ga magoya bayansu da 'yan Najeriya gaba daya da a yi taka tsantsan da irin murnar da za'a yi domin kada a cigaba da asarar rayuka.
A kan haka ne tuni wadansu 'yan Najeriya suka dukufa wurin jawo hankalin jama'ar kasa na daukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da cewa irin wadannan matsaloli basu bazu ba. Kada kuma a yi anfani da murnar a tunzurawa wadanda basu yi nasara ba a zaben.
Wani mai sharhi Alhaji Abubakar Ali yana gargadi ga 'yan kasa cewa a san irin murnar da za'a yi kada a shiga cikin matsala kuma. Yace nasarar ba ta APC kadai ba ce ta duk 'yan Najeriya ne. Saboda haka idan za'a yi murna kada a yi wacce zata kawo barna. Murna ta farko ita ce a godewa Allah an yi zabe lafiya. Ta biyu magoya bayan Buhari su gode dan takararsu ya samu nasara. Wadanda basu samu nasara ba a basu hakuri a kuma rungumi juna.
Yace wasu a cikin murnar su kan tada rikici domin cimma muradunsu. Saboda haka idan suna kaunar Buharin ne su yi addu'a Allah ya bashi ikon yin mulkinsa cikin zaman lafiya.
Shi ma Sanata Sodangi Danso yace yakamata a yi taka tsantsan domin kada murna ta koma ciki saboda wadanda basu bi kai'doji ba ko irin murnar da zasu yi.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.