Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batutuwan Da Buhari Zai Sa Gaba - Namaiwa


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Mutane a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da abin da zababben shugaban kasar Najeriya janar Muhammadu Buhari ya kamata ya tunkura bayan lashe zaben da ya yi a karshen makon da ya gabata.

Yanzu haka mutanen Najeriya da sauran yankunan Afrika na ta fadin albarkacin bakinsu kan inda ya kamata sabuwar gwamnatin Najeriya ta sa gaba

A farkon makon nan hukumar zabe ta bayyana Janar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon da ya gabata inda ya ka da shugaba mai ci Dr. Goodluck Jonathan.

“Na farko shi ne zaman lafiya ya dawo a cikin Najeriya, wato wannna matsala da ke gare mu ta Boko Haram, ya shawo kanta, na biyu matsalar zaman kashe wando na uku a dinga adalci a cikin iko.” In ji Farfesa Boube Namaiwa na jami’ar Cheikh Anta-Diop da ke Dakar a Senegal.

Farfesan ya kara da cewa, akwai bukatar Buhari ya tunkari batun cin hanci da rashawa a kasar sannan ya tuna cewa ta hanyar kuri’u ya samu mulki ba ta hanyar juyin mulki ba duk da cewa yaki da rashawa na bukatar irin jajircewar da ya nuna a farko.

“Muddin dukka wadannan suka samu, to Najeriya za ta zama daya daga cikin kasashen duniya masu fada a ji.” In ji Farfesa Namaiwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG