Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Zata Hana Ta'adanci da Cin Hanci da Rashawa


Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammad Buhari

Yayinda yake karbar takardar shaidar lashe zabe Janar Buhari yace yanzu ne a karon farko aka yiwa 'yan Najeriya zaben adalci inda kuri'unsu suka yi tasiri.

Janar Buhari yace gwamnatinsa zata dage wajen hana ta'adanci da kuma cin hanci da rashawa da yace sun fi komi ma muni wajan karya kasa.

Janar Buhari yace ya gaya masu sai sun kama madafin iko kana zasu ga iyakar barnar da aka yi. Ya yi alkawarin yin iyakar kokarinsu su gyara.

A wani bangaren kuma shugaban hukumar zabe Farfasa Attahiru Jega na farin cikin kammala zaben lami lafiya ya kuma hada da cewa shi bai fuskanci wata takurawa ba kamar yadda ake ta rade-radin fada. Yace duk wani batun cewa ana neman a tursasa masa ko ya yi magudi tsakani da Allah duk basu faru ba. Banda haka yace duk abun da suka ce suna nema da zai taimakawa aikinsu an basu.

Jami'iyyar PDP ta bakin sakataran kwamitin amintattu Sanata Walid Jibril yace haka Allah ya hukunta. Yace karbar sakamakon zaben da yadda da zaben Janar Buhari ya zama shugaban kasa ya kashe wasu abubuwa da dama. Yace ba dan shugaba Jonathan ya yi maganar da ya yi ba da yau ana cikin tashin hankali. Da an yi murdiya da kasar tana cikin mummunan tashin hankali. Yace a yi hakuri a yi nadama a kara karfin gwiwa saboda su sake gina jam'iyyarsu ta PDP.

Yanzu dai kungiyogi da dama na nuna muba'aya ga Janar Buhari wanda zai karbi ragamar mulki a hukumance watan gobe. Misali kungiyar kwadago ta raba takardar goyon bayan shugaban tana bada tabbacin yin aiki dashi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG