Al'ummomin Borno da Yobe sun kira sabon shugaban ya yiwa Allah ya kawar masu da matsalolin da suka fada ciki yau fiye da shekara biyar.
Babbar matsalar da suke fama da ita ce ta rigingimun Boko Haram da suka karya tattalin arzikin yankin ya kuma tarwatsasu sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kai masu.
Ambassador Ahmed Jidda babban sakataren jihar Borno yace su mutanen Borno da Yobe da Adamawa suna murna da aka basu daman jefa kuri'a su zabi wanda suke so. Yace dama mutanen Borno suna da abun dake damunsu. Sun kwashi shekaru biyar suna fama da tashin tashinar Boko Haram. Suna neman a zo a taimaka masu a kuma tallafa masu domin kare kansu daga matsalar. Yace amma ba'a yi masu ba.
Yace koda ma an so a yi masu lokaci ya riga ya kure. Mutane sun hasala shi ya sa suka fito suka nuna fushinsu da yadda suka yi zabe. Suna neman shugaban kasa wanda zai kawar masu da Boko Haram, kungiyar da ta hanasu sakat, ta hanasu rayuwa, ta hanasu mulki, ta kuma rabasu da muhallansu tare da kashe dubun dubatansu.
Yace Janar Buhari ya san sun taimaka mashi. Saboda haka daga ya hau kan mulki ranar 29 ga watan Mayu abun da zai yi masu shi ne ya gama masu da Boko Haram.
Sun kira Janar Buhari ya taimaka masu da gaggawa domin su fito daga kangin Boko Haram. Haka ma 'yan Yobe sun kira sabon shugaban ya kwato kasar daga irin kangin da ta shiga musamman yankin arewacin Najeriya.Tattalin arzikinsu ya durkushe fiye da yadda ake zato.
Daga karshe sun jawo hankalinsa ya guji wasu mugayen mashawarta da ka iya karkata hankalinsa daga abun da ya kamata ya yi.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.