Yayin da ‘yan Najeriya ke cigaba da bukukuwan lashe zaben 2015 da jam’iyar APC tayi, rahotanni sun nuna cewar kasashen duniya dan-daban sun taka rawar gani wajan samun nasarar yin zabe cikin kwanciyar hankali da kiyaye doka.
A hirar wakilin sashin Hausa Irahim Ka’almasih Garba da Malam Aminu Sule, shugaban kungiyar (Network for Justice) kuma mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum, yayi Karin bayanin cewar kungiyoyi da kasashen duniya musamman Amurka sun taka rawar gani a lamabin.
A cewar sa, kasashen sun taimaka ma Najeriya da shawarwai da kuma kayan aiki domin cimma wannan kyakkyawar maunfa wato ta neman dorewar demokaradiyya a kasar.
Kasar Amurk da takwarata ta ingila sun fito karara suka fadi cewar bazasu yadda da duk wani magudin zabe ba, dalilin hakan ya nuna cewar suna da wakilansu a ko ina kuma hakan ya taimaka kwarai.
Yayi Karin bayanin cewa akwai kuma taimakkon da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya na cikin gida sun taimaka kwarai, misali kungiyar mata da ta sayi ruwa ta rarrabawa mutane a lokacin zabe.
Daga karshe kuma shi kanshi shugaba Goodluck Jonathan yayi kokari musamman ta yadda ya fito ya nuna dattako, harma ya kira zababben shugaban domin taya shi murnar lashe zaben. Haka ma kafafen yada labaru, a cewar mai fashin bakin “sai dai muce masu Allah ya saka da alheri domin sun taimaka kwarai.’