Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Tace Ko Kusa Kasar Ba Zata Zama Dandalin Kitsa Rikici A Ivory Coast


Shugaban Ghana John Attah Mills,lokacinda ya kai ziyara Najeriya domin taron ECOWAS
Shugaban Ghana John Attah Mills,lokacinda ya kai ziyara Najeriya domin taron ECOWAS

Shugaban kasar Ghana John Atta Mills yace ba zai bar kowa yayi anfani da kasarshi ba wajen kitsa wani sabon rikici a makwapciyar kasar Ivory Coast.

Shugaban kasar Ghana John Atta Mills yace ba zai bar kowa yayi anfani da kasarshi ba wajen kitsa wani sabon rikici a makwapciyar kasar Ivory Coast.

Mr. Mills yana maida murtani ne ga rahottanin da wasu jaridun Ghana suka bada na cewa akwai wasu giggan mukkaraban tsohon shugaban Cote d’Ivoire, Laurent Gabgbo zaune a cikin Ghana. A lokacinda yake ban kwana ga jakadan Ivory Coast mai barin gado, Emmanuel Ackah a jiya Litinin ne, shugaban na Ghana yake cewa ba wani shugaba da ya san ciyon kansa da zai kyale a yi anfani da kasarsa wajen janyowa wata kasa tarzoma.

Mr. Mills yace Ghana na son ganin zaman lafiya ya dawo a Ivory Coast, ya kuma lura da yadda tashin-hankalin da ya barke a kasar ya ingiza dubban mutanen Ivory Coast din gudowa, suna kwarara zuwa cikin Ghana. Shugaban na Ghana yace yana aiki da sabon shugaban Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara wajen neman sulhunta wannan rikicin na Ivory Coast.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG