Babbar Kotun Kasa da Kasa ta shari’ar manyan laifuka ta bukaci alkalai su bayar da sammacin kama shugaban Libiya Muammar Gaddafi, da daya daga cikin ‘yayansa da shugaban hukumar leken asirin kasar, bisa laifin take hakkin dan adam.
Luis Moreno-Ocampo ya fadi a birnin Hague a jiya Litini cewa Mr. Gaddafi da Saif al-Islam Gaddafi da shugaban hukumar leken asirin kasar Abdullah al-Sanousi sun aikata laifin da zummar tabbatar da dorewar mulkin shugaban na Libiya.
Masu gabatar da kara na Kotun ta kasa da kasa sun ce bayanai sun nuna cewa Mr Gaddafi da kansa ya bayar da umurnin kai harin kan fararen hula tun bayan day a kaddamar da mummunar yinkurin murkushe tawayen kin gwamnati a watan Fabrairu.
Alkalai za su yi nazarin bayanan sannan su amince da bukatar sammacin ko su yi watsi da ita ko kuma su bukaci karin bayanai. Ana kyautata zaton matakin zai dauki makwanni.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Libiya Khaled Kaim ya yi watsi da hanzarin na Kotun ta kasa da kasa, da cewa akwai ayar tambaya a kai.
A halin da ake ciki kuma, wasu jiragen yaki a karkashin ikon NATO sun kai hari kan wasu gine-ginen gwamnati biyu a tsakiyar birnin Trabulus da safiyar yau Talata su ka kama da wuta. Daya daga cikin gine-ginen hukumar leken asirin kasar ce ke amfani da shi, dayan kuma hedikwatar kumar yaki da rashawa da cin hanci ce.
An ji karar a kalla fashe-fashe uku da ake kyautata zaton hare-haren NATO ne su ka haddasa a kusa da gidan Gaddafi da ke Trabulus a ran Litini.
NATO ta kaddamar da hare-hare na kulluyaumin a birnin Trabulus da zummar karya lagwan Mr. Gaddafi.