Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda Tana Barazanar Hana Jagoran 'Yan Hamayyar Kasar Komawa Kasar


Shugaban 'yan hamayya a Uganda Kizze Besigye da isar sa Kenya domin jinya.
Shugaban 'yan hamayya a Uganda Kizze Besigye da isar sa Kenya domin jinya.

Jagoran ‘yan hamayyar kasar Uganda, Kizza Besigye yace an hana shi shiga jirgin sama da zai taso daga kasar Kenya zuwa Uganda.

Jagoran ‘yan hamayyar kasar Uganda, Kizza Besigye yace an hana shi shiga jirgin sama da zai taso daga kasar Kenya zuwa Uganda, kwana guda kafin bikin rantsar da shugaba Yoweri Museveni zagaye na hudu a matsayin shugaban kasa.

A yau laraba, Besigye yace wani jami’in kamfanin jirgin saman Kenya Airways ya shaiada masa cewar Gwamnatin Uganada tacae ba zata baiwa jirgin saman fasinja iznin sauka ba idan har aka bari Besigye ya shiga jirgin saman. Amma jami’an Gwamnatin Uganda sun musanta wannan zargi, suka ce babu hannun Gwamnatin Uganda a harkokin jigilar jiragen saman fasinja.

Besigye, yaje kasar Kenya ne domin neman magani inda aka kwantar dashi a wani asibitin birnin Nairobi inda ake kula da ciwon aka ji masa a dalilin gwabzawar da suka yi da ‘yan sanda a lokacin kokarta jagorancin yin zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Uganda. Mutane akalla takwas ne suka halaka, sannan sama da mutane metan da hamsin suka jikkata.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG