Ministan harkokin tsaro na kasar Sudan ya yi watsi da kiraye kirayen da ake yi na janye dakarun kasar daga yankin Abyei da ake mummunar takaddama a kai. Membobin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci dakarun da su fice daga Abyei da kudancin Sudan da ke dab da samun ‘yancin kai, da kuma arewacin ke ikirarin mallaka. Ministan tsaron Abdelrahim Mohamed Hussein ya shaidawa ‘yan majalisa yau Litinin cewa Abyei zata ci gaba da kasancewa karkashin arewacin kasar har zuwa lokacin da za a tsaida shawara a kai . Dakarun arewacin Sudan sun kwace ikon yankin ne kwanaki biyu da suka shige bayan da ‘yan bindiga suka kaiwa ayarin sojojin arewacin hari. Bisa ga cewar arewacin kasar, an kashe sama da sojoji 20 a harin da suke zargin dakarun kudancin kasar da kaiwa. Yau Litinin ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Sudan yace mutane dauke da makamai suna kone kone da kwasar ganima a garin Abyei. Kungiyar likitoci ta kasa da kasa Doctors Without Boarders tace akasarin mutanen garin sun kaurace zuwa kudancin kasar. Kwace ikon Abyei da arewacin kasar ya yi, ya sa fargaban barkewar wani sabon yakin basasa a Sudan.
Ministan harkokin tsaro na kasar Sudan ya yi watsi da kiraye kirayen da ake yi na janye dakarun kasar daga yankin Abyei .