Pakistan tayi anfani da harshe mai kaushi wajen yin korafi ga rundunar sojan Turai ta NATO kan abinda Pakistan tace taka dokokinta na sararin samaniya ne wasu bakin jiragen sama biyu masu saukar ungulu suka yi, da suka ratso cikin kasar.
Wannan kokarin yazo ne sa’oi kadan bayanda jami’an Pakistan suka yi zargin cewa wafanan jiragen biyu sun ratso daga Afghanistan zuwa cikin Pakistan, suka kawo farmakin da ya raunana wasu sojoji biyu na Pakistan din. NATO ta tabattarda cewa lalle akwai wasi jiragenta dake sintiri akan kusa da kan iyakar kasashen biyu kuma zata gudanarda bincike a kai.
Wannan al’amarin ba shakka zai kara tsananta zaman dar-dar da ake tsakanin Pakistan da Amurka duk da ziyarar da dan majalisar dattawan Amurka Senator John Kerry yake kaiwa a can Pakistan da fatar sulhunta kasashen biyu.
Farmakin ba-zata da sojan Amurka suka kai a garin Abottabad na Pakistan ran 2 ga watan Mayu, inda suka kashe madugun al-Qaida OBL, ya haifarda cece-kuce sosai a tsakanin kasashen biyu.