Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau aka rantsar da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni a wa'adi na hudu


Leader of the opposition party Forum for Democratic Change Kizza Besigye, background center right, beside his wife Winnie Byayima, left, waves to large crowds of supporters as he returns from Nairobi after medical treatment.
Leader of the opposition party Forum for Democratic Change Kizza Besigye, background center right, beside his wife Winnie Byayima, left, waves to large crowds of supporters as he returns from Nairobi after medical treatment.

Shugaban masu haiyamar kasar Uganda Kizza Besigye ya oma kasarsa Uganda a yayinda ake bikin rantsar da shugaba Yoweri Museveni a wani wa'adin mulki na hudu. Shugaban kasashen Afrika guda bakwai ne suka halarci bikin rantsuwar.

Yau Alhamis ce shugaban masu hamaiya na kasar Uganda Kizza Besigye, ya koma kasar, a dai dai lokacinda ake rantsar da shugaban kasar Yuweri Museveni, a wa’adin mulki na hudu.

Dubban magoya bayan Besigye ne suka tarbeshi a babban tashar jiragen sama ta Entbbe, kwana daya bayan da kamfanin jiragen fasinja ta Kenya ta hana shi komawa gida.

Shaidun gani da ido sun ce sai dai ‘yansanda suka harba borkono tsohuwa, a yayinda gungun jama’a suke bin jerin gwanon motocin da suke dauke Mr. Besgiye, a yayinda suke barin filin saukar jiragen saman.

A babban birnin Kasar Kampala kuma, dubban mutane ne suka halarci bikin rantsar shugaban Yuweri Museveni, domin fara sabon wa’adin mulki na tsawon shekaru biyar.

Shugabannin kasashen Afirka bakwai ne suka halarci bikin, amma banda na Sudan, Omar al-Bashir, wanda aka gaiyata to amma kuma kamar yadda aka sani, kotun dake shari'ar manyan laifuffukan yaki ta kasa da kasa ta bada umarnin a kama shi, saboda ya amsa tuhuma da take masa

XS
SM
MD
LG