A Masar kuma masu gabatar da kara sunce anyi wa tsohon shugaba Hosni Mubaraka da uwargidansa Suzanne tambayoyi akan zargin tara dukiya mai dumbin yawa ta hanyoyin da basu dace ba.
Jami’ai suka ce yau Alhamis ce aka yi wa shugaban da uwargidansa tambayoyi a birnin Sharm el-sheikh, inda ake yiwa jinyar Mr. Mubarak jinya, bayan da aka hambarar gwamnatinsa sakamakon zanga zangar kin jinin gwamnatinsa da aka yi cikin watan janairu da febwairu. Akwai rahotannin dake cewa tsohon shugaban yana fama da ciwon zuciya da wasu matsaloli. Haka ma hukumomin kasar suna binciken ‘ya’yan tsohon shugaban kasan.