Saboda haka tsofaffin kwamishinonin sun nemi fadar shugaban kasa da jam’iyyar PDP su saka baki dangane da abunda suka kira halin “ni ‘yasu”, da suka ce jihar ke ciki.
Mr. Usman yace “a yi wani abu dangane da abunda shi mataimakin gwamnan Taraba yake yi. Idan ba’a yi wani abu game da abubuwan da yake yi ba, to a gaskiya PDP zata samu damuwa a jihar Taraba. Don abunda yake yi, zai rusar da Taraba, kuma baza mu so hakan ya faru ba.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba, Mr. Jibril Adoneji ya mayar da martani ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda jihar DSP Joseph Koji ya musanta zargin da kwamishinonin, yana mai cewa zargin bashi da tushe balle makama.
“Ba gaskiya bane, ba gaskiya bane. Wannan ma bansan da wannan maganar ba”, inji DSP Koji.
“Mu namu shine, idan lokacin zabe yazo, zamu tabbatar ‘yan sanda sunje sun kula da wannan zaben, a tabbatar an yi zabe, kuma an gama lafiya.
Shima mukadashin gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar, ta bakin sakataren yada labaransa Mr. Sule Kefas ya musanta wannan zargi, inda yace shi kullum biyayya yake wa maigidansa Danbaba Suntai, kuma ya musanta zargin da ake masa na cewa yana amfani da ‘yan sanda wajen musgunawa abokan hamayyarsa.
“Wannan magana, ba haka take ba. Gaskiyar magana, kowa ya san cewa shi maigirma mukaddashin gwamna, mai biyayya ne ga maigidansa Danbaba Suntai”, inji Mr. Kefas.
“Shirin da aka yi, domin a samu zaman lafiya, a yi wannan abu bada tashin hankali ba. To wannan magana kuma, zan fadi cewa ra’ayi ne, babu gaskiya a cikin wannan magana,” Mr. Kefas ya kammala.
Yanzu haka ana haramar zaben cike gurbin a mazabar Takum, mazabar da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar ya fito, kuma rasuwarshi ta bude wani shafi a dambarwar siyasar jihar, inda bangarori biyu ke kokarin nuna bajinta.