Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Taraba ta Musanta Yiwa Gwamna Suntai Daurin Talala


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Dambarwar siyasa a jihar Taraba sai sake salo ta keyi inda yanzu wasu na hannun daman gwamna Danbaba Suntai suna zargin mukaddashinsa da yi masa daurin talala

Mukaraban gwamna Danbaba Suntai suna zargin mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar da yiwa gwamnan daurin talala a gidan gwamnati.

Idan dai ba'a manta majalisar dokokin jihar Taraba bata yadda gwamna Danbaba Suntai ya koma bakin aikinsa ba sabili da rashin lafiya. Yayin da majalisar ta umurceshi ya koma cigaba da yin jinya ta aiwatar da dokar da ta ba mukaddashinsa Alhaji Garba Umar izinin cigaba da rike madafin ikon mulkin jihar.

Tun gada lokacin a kaitakai ruwa rana tsakanin mutanen gwamnan da na mukaddashinsa. Kamar sau biyu mutanen Suntai, wanda har yanzu ba'a ganshi a bainar jama'a ba kuma shi kansa bai yiwa kowa jawabi ba, suka yi kokarin mayarda shi kan mulki ta bayan fagge. Kawo yanzu dai majalisar ta tsaya kan bakanta.

A wata takarda da mukaraban gwamna Danbaba Suntai suka fitar a karkashin kungiyar dake fafitikar kare jihar sun zargi mukaddashin gwamnan da yiwa Danbaba Suntai daurin talala inda suka ce yanzu haka ya hana kowa ganin gwamnan. Sanato Emmanuel Bacha mai wakiltar kudancin Taraba wanda kuma yake kan gaba wurin dawo da gwamnan daga Amurka inda yake jinya yana cikin masu yin wannan sabon zargin.Ya ce tunda mukaddashin gwamnan ya yi kokarin kwace mulki daga hannun gwamnan amma bai ci nasara ba to tsoronsu yanzu shi ne yana iya anfani da daurin talala ya kashe gwamnan.

Ta bakin Sanato din ban da hana mutane ganin gwamna Suntai ya ce sun samu labari mukaddashin yana can-canza jami'an tsaron gidan gwamnati wasu kuma yana cusa masu kudi. Amma wai suna addu'a Allah ya yiwa gwamnan kariya.

Mukaddashin gwamnan ta bakin kakakinsa Sule Cefas ya ce batun ba haka yake ba kuma babu kashin gaskiya ciki. Ya ce sau dayawa mukaddashin gwamnan ya sha fada cewa gwamna Danbaba Suntai maigidansa ne. Kuma har gobe matsayin mukaddashin ke nan sabili da haka ta yaya zai nemi ya yi masa daurin talala ko ya nemi ya hallakashi?

Yanzu dai an sa ido a ga yadda zata kaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG