Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Juyayin Rasuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Bayan an bayyana rasuwar kakakin majalisar dokokin jihar Taraba kama daga mukaddashin gwamnan jihar zuwa mazauna gari sai juyayin wannan lamarin a keyi.

Babu zato babu tsammani aka bayyana rasuwar kakakin majalisar dokokin jihar Taraba Mr. Haruna Tsokwa.

Bayan an bayyana rasuwar Mr. Haruna Tsokwa to ko menene ya biyo baya. Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya zagaya ya jiwo ya kuma gani ma idanunsa. Ya ce yanzu koina ka duba a jihar zance guda ake yi, wato rasuwar kakakin majalisar dokokin jihar. Tuni har mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar ya kai gaisuwar ta'aziya zuwa gidan marigayin.Kamar yadda mukaddashin kakakin gwamnan Mr. Kefas Sule ya fada a wurin ta'aziyar, wani babban rashi a ka yi a jihar. Ta bakin Kefas Sule mukaddashin gwamnan ya gayawa iyalan mariyayin cewa abun da ya faru abun mamaki ne domin kwanaki biyu da suka wuce suna tare dashi. Babu wani alamar cewa dan jiwon da yake fama da shi zai kai ga rashin ransa yau.
Ya ce idan Allah ya yi abunsa babu abun da mutum zai iya yi. Mukaddashin gwamnan ya roki kowa ya yi hakuri.

Kafin rasuwarsa Haruna Tsokwa ya bayyana irin halin da suka samu gwamna Danbaba Suntai lamarin da ya sa su goma sha shida suka ga yakamata su barshi ya koma jinya shi kuma mukaddashinsa ya cigaba da rike madafin iko. Domin yin hakan shi ne gaskiya ba wai saboda wani mutum ba ko son kai ko kuma domin son abun duniya.

Yawancin 'yan jihar da aka zanta dasu sun ce rasuwar kakakin wata babbar rashi suka yi a jiharsu musamman a wannan lokacin da majalisar ke shirin tantance sabbin kwamishanoni da kuma hankoron abun da ka faru a siyasar dake zuwa. Rashin, inji wasu, tamkar mayarda hannun agogo baya ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG