Amma da alama 'yan koran gwamna Danbaba Suntai ba zasu hakura ba sai gwamnan ya koma bakin aikinsa. Kwasam sai gashi wasu tsofofin kwamishanoni na jihar karkashin mulkin Suntai da suka hada da tsohon kwamishanan kudi Mr. Rabo Usman sun kirawo taron manema labarai inda suke zargin mukaddashin gwamnan da yin anfani da 'yansanda wajen musgunawa wadanda suke tare da su. Mr Rabo na nufin duk wadanda suke kan gaban komo da gwamna Danbaba Suntai mukaddashin gwamnan ya sasu gaba. Sabili da hakan sun kira fadar shugaban kasa ta sa baki domin halin ni'yasu da suka ce jihar ke ciki.
Mr. Rabo ya ce a yi wani abu game da abun da mukaddashin gwamna ke yi. Ya ce idan ba'a yi wani abu ba PDP zata samu damuwa a jihar. Abun da mukaddashin gwamnan ke yi injishi zai rusa PDP a Taraba. Ya ce ba zasu so wanda bai san aikin da suka yi ba kafin jam'iyyar ta kafu ya zo ya rusa masa ita. Shugabannin PDP a tarayya su duba abun dake faruwa tsakanin gwamnan da mukaddashinsa.
To sai dai kwamishsanan 'yansandan jihar Mr Jibril Adeniji ta bakin kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Joseph Kwaji ya musanta zargin ya ce bashi da tushe bare makama. Ya ce nasu aikin shi ne lokacin zabe su tabbatar da tsaro a gama lafiya.
Mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar ta bakin sakataren yada labaransa Mr. Sule Kefas ya musanta zargin inda ya ce kullum mukaddashin biyayya ya keyi ga maigidansa Danbaba Suntai domin haka ya roki jama'ar jihar kada su bari 'yan tada fitina su tunzurasu.