Tun bayan komo da shi daga kasar Amurka inda yake jinya bayan wani mugun hatsarin jirgin sama da ya samu, gwamnan bai bayyana a bainar jama'a ba haka kuma bai ce uffan ba sai a wannan karon.
A wani bidiyo da ya fitar gwamnan ya godewa Allah da lafiyar da yake samu. Ya kuma shawarci 'yan Najeriya su koma ga Allah. A cikin tausassar murya gwamnan ya ce yanzu ba zai iya komawa ofishinsa ba. Amma yana rokon a taimaka masa domin a akasarin gaskiya baya cikin koshin lafiya ko kadan. Ya ce bashi da koshin lafiya da zai sa ya kama aiki domin wani ya goyi bayansa. Babu. Lafiya yake bukata ba komawa ofis ba.
A wani lamari na baiwa 'yan Najeriya shawara musamman masu son yin anfani da shi domin cimma muradun kansu gwamna Suntai ya yi gargadin su koma ga Allah shi ne ya fi. Idan sun yi haka zasu magance duk wadannan matsaloli domin Allah baya son ayyukan asha amma muna aikatawa duk da munsan Allah bai ce mu aikata ba. Ya ce abun takaici ne muna sauraren Shaidan a wannan lamari. Abun bakin ciki ne muna jefa kanmu cikin shan barasa. Gwamnan ya ce yana fata jama'a zasu daina.
Amma masu kula da harkokin yau da kullum suna ganin akwai abun dubawa a firar da gwamnan ya yi. Sanato Muhammed Ibrahim Goje wanda yana cikin kungiyar cigaban jihar Taraba ya ce tun da gwamnan ya fada da bakinsa ba zai iya komawa bakin aikinsa ba ya kamata yanzu mutanen Taraba su kai zuciya nesa. Ya kamata a bi gaskiya a yi abun da ya kamata.
Shi ma mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Umaru Garba ta bakin kakakinsa Kefas Sule ya kira 'yan jihar su hada kai domin su yi aiki tare. Ya ce gaskiya nada mahimmanci. Dole a aikata gaskiya domin ita ce komi. Idan aka tsaya kan karya akwai lokacin da asiri zai tonu. Duk abun da mutum zai fada ya tabbata gaskiya ne.