Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Taraba Ta Samu Sabon Kakaki


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Bayan rasuwar kakakin majalisar dokokin jihar Taraba makon jiya yanzu ta samu sabo

Idan dai ba'a manta ba makon da ya wuce ne Mr. Haruna Tsokwa kakakin majalisar dokokin jihar Taraba ya rasu lamarin da ya kai ga zaben wani ya maye gurbinsa.

Majalisar ta yi zamanta ne cikin tsauraran matakan tsaro inda shugabannin majalisar na da suka gana a kebe na wani dan lokaci.

A zaben da suka gudanar shugaban masu rinjaye da ya fito daga kudancin jihar Josiah Sabo Kinte tsohon dan jarida shi ne ya zama sabon kakaki. Shi kuma Tanko Maikarfi da ya tsallake rijiya da baya a wani kokarin harbeshi ya cigaba da zama mataimakin kakakin majalisar.

A jawabinsa mataimakin kakakin majalisar ya kira 'yan jihar su yi hakuri da juna kada su dinga sauraren mahaukata masu son tada zaune tsaye. Ya ce shi ya san 'yan Taraba masu ladabi ne kuma masu addini ne. Ya ce Allah ke ba mutum mukami ba yadda wasu suka dauka ba.

Wasu 'yan kallo sun ce sun zo majalisar ne domin siyasar jihar ta zama abun jita-jita. Sun zo su gane ma idanunsu abunbuwan dake faruwa kamar yadda Christopher John ya fadawa wakilinmu. Ya ce sun ji dadin yadda aka yi zaben. Sun yi fatan za'a samu cigaba ba kamar yadda abubuwa suka tsaya tsit ba a da.

Haka ma majalisar ta karanta sunayen mutane shida da za'a nada kwamishanoni. Ta ba da tabbacin tantancesu gobe Talata.

Ga karin rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG