Idan ba'a manta ba lokacin da gwamnan ya samu hadarin jirgin sama da shi kanshi ke tukawa a kaishi kasar waje domin a kula da lafiyarsa. Ya yi wata da watanni kafin ya dawo a cikin wani halin rudani. Ko da ya dawo an ce baya cikin koshin lafiya har wai baya iya gane mutane. Akasarin gaskiya ma tun da ya dawo babu wanda ya ganshi a bainar jama'a kuma kawo yanzu bai taba fitowa ya yi jawabi da manema labarai ko wadanda suka je gaisheshi. Lamarin da ya sa kenan majalisar dokokin jihar ta amincewa mataimakin gwamnan Umaru Garba ya cigaba da mulkin jihar a matsayin mukaddashin gwamnan.
Da alamu na kusa da gwamnan basu ji dadin matsayin majalisar ba shi ya sa suna ta yin kokarin mayarda gwamnan kan karagar mulki ko ta halin kaka. Wannan yunkurin baya bayan nan shi ne na uku to amma ko shi ma ya cutura domin 'yan majalisar dokokin jihar suna nan kan bakansu na cewa gwamnan ya koma ya cigaba da yin jinya.
Masana harkokin siyasa da shari'a sun yi furuci kan kokarin baya bayan nan. Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Tanko Maikarfi ya rantse ya ce suna nan kan ra'ayinsu. Mukaddashin gwamna ya cigaba da aikinsa. Ya kira jama'ar Taraba su yi hankali da mutanen da ke kokarin yin anfani da gwamnan. Ya ce muradun kansu suke son su cimma ba wai suna son gwamnan ba ko ita jihar. Ya ce kansu kawai suka sani. Amma su a majalisa suna kan matsayin da suka riga suka tsayar.
Barrister Solomon Dalung ya ce akwai bukatar kafin ta natsu a jihar Taraba. Ya ce duk wadanda suke jigila da gwamna Suntai suna neman su mayarda shi kan karagar mulki su ne manyan munafukai. Ya ce gwamna Suntai ya zama kayan gwamnatin Taraba domin bashi da isasshen lafiya. A karkashin doka shugaban kasa bashi da iko ya mayarda Suntai kan karagar mulki sai abun da doka ta tanada da abun da majalisar jihar ta yi.
Ga karin bayani.