Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fulani Sun Baiwa Sojoji Gudunmawar Shanu


Shanun Fulani.
Shanun Fulani.

Gudumawar sun hada da Shanu 29, buhun Shinkafa 50, man girki kwallaye 20, da buhuhuwan gishiri 20

Kungiyar hadin kan Fulani Bororo, na kasar jamhuriyar Kamaru, da ake kira Buskuda, sun baiwa dakarun jamhuriyar Kamaru gudumawar Shanu 29, buhun Shinkafa 50, man girki kwallaye 20, da buhuhuwan gishiri 20, domin kara masu kwarin gwiwa na yaki da suke yi da kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram.

Wanna kyauta dai sun mikawa magatakardan Ministan harkokin cikin gida ta jamhuriyar Kamaru ne,gudunmawar dai shugaban kungiyar Buskuda ne na kasar ta jamhuriyar Kamaru, Alhaji Manu Jaji Gidaddo, shine ya mika wannan gudumawar.

Ya ce matan mu da mazan mu da dabbobin mu mayakan Boko Haram sun kwashe su sun kai su cikin daji tsakanin jamhuriyar Kamaru da kasar tarayyar Najeriya, ya ce duk ‘ya’yan wanna kungiyar ta Buskuda na lale marhaba da irin aikin da Sojojin kasar ta jamhuriyar Kamaru keyi domin cimma burin zaman lafiya a kasar baki daya.

Shima magatakardan ya ce wannan abun arziki da ‘yan Buskuda suka kawo za’a mika shi ga inda ya dace kuma ya ce yana fata sauran kungiyoyi za suyi koyi da iri wannan kyawawan dabi’u.

Wanna kungiya dai ta hadin kan Fulani wace ake kira Buskuda a dunkule suna gwagwarmaya ne na nemawa Fulani Bororo ‘yancin su masamman ma wajen samar masu da ilimi na zamani dana addini don cewar kar abarsu a baya wajen ci gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karo na biyu kenan a Nijar ake gudanar da bukukuwan Kirsimetin karkashin mulkin soja, inda a bara takunkumin ECOWAS ya dakushe farin cikin
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG