Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Harba Makamai Masu Linzami daga Tekun Baharum Zuwa Sansanin ISIS


Vladimir Putin Shugaban Kasa Rasha
Vladimir Putin Shugaban Kasa Rasha

Rasha ta ce a karon farko ta yi nasarar kai hari akan wata tungar ‘yan kungiyar ISIS a arewacin Syria, bayan da ta harba wasu makamai masu linzami daga karkashin Tekun Meditareniya.

Da yammacin jiya Talata ne, Ministan tsaron Rasha, Sergie Shoigu, ya gayawa shugaba Vladmir Putin ta kafar bidiyo cewa dakarun kasar sun kaikaici wasu wurare biyu da ‘yan kungiyar IS ke boye makamai a birnin Raqqa na Syria.

Ministan Tsaron ya ce, “Mun yi imanin cewa mun lalata wasu rumbun makaman mayakan IS da kuma wani wuri da suke hada nakiyoyi hade da adana mai a kusa da iyakar Turkiyya.”

Ya kuma kara da cewa akalla mafakar mayakan IS guda 600 aka kai hare-hare cikin kwanaki uku da suka gabata.

Wannan rahoto da ministan tsaron kasar ya gabatarwa shugaba Putin ta kafar bidiyo, na zuwa ne a daidai lokacin da kafofin yada labaran Rasha suka ruwaito cewa Rashan da Syria sun kammala kwashe baraguzan jirgin kasar samfurin SU-24 da aka harbo a iyakar Turkiyya.

Rasha dai ta fara kai hare-haren sama ne a Syria a karshen watan Satumba domin tallafawa gwamnatin Bashar- al Assad, kasancewar Syria babbar kawar Rasha ce.

Amurka dai da kawayenta na ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren saman da Rashan ke kaiwa, inda suke ikrarin cewa shugaba Putin na karawa gwamnatin Assad karfi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG