A halin da ake ciki, Amurka na duba wani rahoto da ke nuni da cewa Iran ta gudanar da wani gwajin makami mai linzami a karshen watan da ya gabata, abinda Amurkan ta ce ya sabawa dokar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
A jiya Talata Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power, ta ce Amurkan na gudanar da binciken kwakwaf kan wannan rahoto, za kuma ta dauki matakan da suka dace, muddin aka tabbatar da sahihancin rahoton.
Jami’an Amurka sun ce a ranar 21 ga watan Nuwamba Iran ta gudanar da gwajin makami mai linzamin, wanda ya yi tafiya a tsakankanin kasar ta Iran.
Jakadar ta Amurka, ta ce sun kudiri aniyar ganin sun kawo karshen ayyukan kasar ta Iran na yunkurin harba makamai masu linzami.
Wannan dai bashi ne karon farko da Iran din ta yi gwajin makamanta masu linzami ba, ko a watan Oktoban da ya gabata ma ta harba wani makamin mai tafiyar dogon zango, lamarin da janyo suka daga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.