Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: Badi Maniyatta Zasu Soma Anfani da Filin Jirgin Saman Jalingo


Yanzu jirgin sama ya fara sauka a Jalingo fadar gwamnatin Taraba
Yanzu jirgin sama ya fara sauka a Jalingo fadar gwamnatin Taraba

Ankwashe fiye da shekaru goma ana gina filin saukan jirginsama a Jalingo fadar gwamnatin Taraba saboda sau tari sai a yi aiki na 'yan watanni kana ayi watsi da wurin shekara da shekaru.

Kafin a samu a kammala filin saukan jiragen sama a Jalingo matafiya Abuja ko Kano ko Legas ta jirgin sama na daukan sa'o'i uku zuwa hudu kafin su kai filin saukar jiragen sama mafi kusa da Jalingo, wato Yola a jihar Adamawa.

Yanzu filin saukan jirgin saman Jalingo ya fara aiki. Wani jirgi ya dauko fasinjoji 48 a gwajin farko daga Abuja zuwa Jalingo. Cikin fasinjojin wani yace da sai sun dauki mota daga Jalingo zuwa Yola, sun yi tafiyar awa uku ko hudu saboda munin hanyar amma yau gashi sun taso daga Abuja kai tsaye zuwa Jalingo.

Samun filin yana aiki zai taimakawa ayyukan kasuwanci. Kasuwanci zai habaka domin maimakon mutane su bata lokaci zuwa Yola yanzu sai su tashi kai tsaye.Rashin hanyoyin mota masu kyau na jawowa harkokin kasuwanci da yawon bude ido cikas a jihar.

Gwamnan jihar yace ya baiwa gina filin fifiko ne domin sauwakawa maniyatta musulmai da kristoci masu zuwa aikin ibada. Haka kuma samun filin zai habaka ayyukan yawon bude ido zuwa wurare kamar su Mambila da Gashaka ko Kashinmila da sauransu.

Zuwa gaba ana iya fitar da albarkatun gona da jirgin sama daga jihar da kuma shigo da kaya zuwa cikin jihar.

Mazauna kauyukan dake kan hanya zuwa Jalingo daga Yola sun roki gwamnatin tarayya da ta sanya gina hanyar cikin kasafin kudi na shekarar 2016.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG