Hukumomin Yamal na sa ran dakarun kasar da ‘yan tawayen Houthi, za su amince da wani shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki bakwai, idan suka hadu a wani taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Switzerland domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Shugaban kasar, Abd Rabu Mansour Hadi, ya aikewa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wata wasika, inda ya bayyana yadda shirin tsagai wutan zai kankama, tare da fatan za a kara tsawaita shirin idan har ‘yan bangaren Houthin suka amince.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin na Yamal, Isma’il Ould Sheikh Ahmed, ya ba da tabbacin cewa bangarorin biyu za su tsagaita wuta na dan wani lokaci, bayan da ya ayyana cewa dukkaninsu sun himmatu wajen ganin an samu maslaha kan rikicin, a wannan zama da za a fara a ranar 15 ga watan Disamba.
Ana dai sa ran, jami’an Majalisar Wakilan kasar dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, suma za su halarci wannan zama.
Rikicin Yamal dai ya halaka akalla fararen hula dubu 2,500 a wannan shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.