Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an fara tuhumar mutanen hudu a birnin Paris, sai dai babu masaniyar ko ana musu tambayoyi ne a matsayin wadanda ake zargi ko kuma wadanda su ke ba da shaida.
Rahotanni sun ce sojojin na Faransa sun aikata laifukan fyaden ne a karshen shekarar 2013 da kuma tsakiyar shekarar 2014, lamarin da bai fito idon duniya ba sai a farkon wannan shekara bayan da Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta wallafa wani rahoto akai.
Bayanai sun ce a bara ne hukumomin Faransa suka samu rahoto kan zargin aikata fyaden, inda suka kaddamar da bincike a kai ba tare da sun fito sun bayyana lamarin ba.
Wannan zargi na fyade da ake yiwa sojojin na Faransa, ya janyo suka sosai kan kasar da ma Majalisar Dinkin Duniya dangane da yadda suke tafiyar da lamarin.