WASHINGTON, D. C. - Hakan kuma ya kawo karshen hadin gwiwar soji da kasar ta yammacin Afirka.
Matakin janye dakaru 1,500 daga Nijar ya haifar da gibi a kokarin da kasashen yammacin duniya ke yi na dakile ayukan tada kayar baya na masu tsattsauran kishin Islama da aka kwashe shekaru goma ana yi. Har ila yau, hakan ya yi mummunar illa ga tasirin Faransa a yankin Sahel kuma zai iya bai wa Rasha damar fadada ikonta a kan manyan wuraren da ba su da tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da ta aka fitar a ranar Alhamis, ma'aikatar tsaron Faransa ta ce sojojin za su koma kasar Faransa kuma za'a kammala kwashe sojojin a karshen wannan shekara.
Nijar dai ita ce babbar aminiyar kasashen yammacin duniya a yankin tsakiyar Sahel da ke kudu da hamadar Sahara har zuwa ranar 26 ga watan Yuli da aka yi juyin mulkin da ya kawo gwamnatin mulkin soja wadda ya bukaci Faransa ta fice daga kasar.
Macron ya kuma janye jakadan kasarsa daga Nijar.
-AP
Dandalin Mu Tattauna