Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Faransa Ya Bar Nijar Yayin Da Dangantaka Tsakanin Kasashen Biyu Ta Yi Tsami


Sylvain Itté
Sylvain Itté

Wasu majiyoyin jami’an tsaro biyu sun ce Sylvain Itte ya ba Nijar ta jirgin sama, labarin da daga bisani ofishin shugaban Faransa dake birnin Paris ya tabbatar.

Jakadan Faransa a Nijar ya bar birnin Yamai da sanyin safiyar Laraba, kusan wata guda bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba da umarnin korar shi, kuma 'yan kwanaki bayan da shugaba Emmanuel Macron ya ce zai janye jami’in diflomasiyyar tare da sojojin Faransa.

Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa, tsohuwar kasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka a baya, wadda ke da rundunar soji a kasar don taimaka wa a yaki da masu ikirarin jihadi, ta tabarbare tun bayan da hafsoshin sojojin kasar suka kwace mulki a Yamai a watan Yuli.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Majalisar mulkin sojan dai ta umarci jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48 a karshen watan Agusta, a zaman martani ga abin da suka bayyana a matsayin matakin da Faransa ta dauka wanda ya saba wa muradun Nijar.

Da farko Faransa ta yi watsi da wannan umarni, inda ta tsaya kan matsayinta na cewa gwamnatin mulkin sojan ba ta bisa doka, tana mai kira da a maido da zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum, wanda aka hambarar a juyin mulkin watan Yuli.

Taron shugabannin kasashen G20 a India
Taron shugabannin kasashen G20 a India

Amma Macron ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa jakadan zai koma birnin Paris, kuma sojojin Faransa za su fice daga kasar da ke yankin yammacin Afrika zuwa karshen shekarar 2023.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG