Emmanuel Macron ya bayyana shirin janye sojan kasar daga yankin Sahel ne saboda a cewarsa, ba za su ci gaba da hulda da gwamnatin sojan da ta yi kane-kane a al’amuran gudanar da mulkin rikon kwaryar kasar Mali ba.
Da yake yi wa manema labarai bayani a game da dalilan daukan wannan mataki, Macron ya alakanta shi da yanayin siyasar da ake ciki a Mali inda sojoji suka yi juyin mulki sau 2 a cikin watanni 9 hujjar da editan jaridar La Roue de l’Histoire Ibrahim Moussa ya ce bai gamsu da ita ba.
A ci gaban bayanansa shugaban na Faransa ya ce duk da yake rundunar Barkhane za ta fice daga Mali, wani rukuni na dakarun kasar za su hade da sojojin rundunar hadin gwiwar kasashen Turai don ci gaba da kafsa yaki da ‘yan ta’adda a iyakar kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali.
Kasar Faransa mai dakaru 5,100 a yankin Sahel na kashe biliyan 1 na Euro a kowace shekara a yakin da aka shafe shekaru kusan 8 a na gwabzawa.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da shi a makon jiya tsohon ministan tsaron kasar Nijar Kalla Moutari ya ce janyewar Faransa daga wannan yaki babbar koma baya ne ga kasashen Sahel.
Kokarin jin ta bakin kakakin wamnatin Nijar Tidjani Abdoulkadri don jin matsayin kasar a game da wannan mataki na hukumomin Faransa, ya ci tura.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: