Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da 'Yan Nijar Ke Cewa Kan Shirin Ficewar Faransa A Kasarsu


Emmanuel Macron
Emmanuel Macron

Shugaban Faransa Hukumomin mulkin sojan Nijar da jami’an fafutuka sun maida martani bayan da shugaban Faransa ya bayyana shirin dauke jakadan kasar daga birnin Yamai zuwa gida.

Haka kuma shugaba Macron a wata hira da kafafen labaran Faransa ya ayyana shirin kwashe dakarun kasarsa daga Nijar kafin karshen shekarar nan ta 2023.

Lamarin da sojojin juyin mulki suka ayyana a matsayin matakin nasara yayin da wasu ‘yan kasar ke cewa za su ci gaba da gwagwarmaya har ranar da Faransar ta fice kwata-kwata daga Nijar.

Sa’oi kadan bayan shugaba Macron ya sanar da shirin dauke jakada Sylvain Itte daga Yamai majalisar CNSP ta bayyana matsayinta akai.

Mahukuntan kasar ta Nijar sun ayyana ranar ta Lahadi da Faransa fitar da sanarwar a matsayin ranar murnar bude sabon babi a yunkurin kwato ‘yancin kan Nijar.

Ficewar jakadan Faransa daga Nijar da maganar kwashe dakarun kasar 1,500 abubuwa ne da al’umma ta shafe lokaci mai tsawo tana na gwagwarmaya akan su.

Tun a ranar 2 ga watan Satumba mazauna birnin Yamai suka tare a kofar sansanin sojIn Faransar don ankarar da su shudewar wa’adin da majalisar CNSP ta ba su.

Jami’in fafutuka ta yanar gizo, Bana Ibrahim wanda ya bayyana farin ciki game da abin da ya kira galaba akan Faransa, ya jaddada aniyar ci gaba da wannan mataki na matsin lamba.

Moustapha Abdoulaye, masani ne a fannin difloamsiya da sha’anin tsaro, ya kuma ce duk da cewa Faransa za ta janye dakarunta, zai iya yiwuwa, idan aka koma mulkin farar hula, Faransa ta sake koma hulda da Nijar.

A shekarar 2015 ne Faransa ta fara girke dakaru a Jamhuriyar Nijar bayan la’akkari da yaduwar ayyukan ta’addanci daga arewacin Mali zuwa sassan jihar Tilabery wanda ke bazanar mamaye Yankin Sahel.

Haka kuma yanayin tsamin dangantakar da aka shiga a tsakanin shugaba Macron da sojojin juyin mulkin Mali ya sa Faransa girke wani bangare na sojojinta kan iyakar kasashen biyu ta bangaren Nijar a bara.

A wani abin da ke kama da ci gaban takun saka, majalisar CNSP a takardar da ta aike wa hukumar sararin samaniya ta ASECNA ta dauki matakin hana wa jiragen Faransa na farar hula da na soja ratsa sararin samaniyar Nijar da nufin tsaurara matakan tsaro.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG