Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Za Ta Janye Dakaru, Jakadanta A Nijar


Emmanuel Macron (AP)
Emmanuel Macron (AP)

Sojojin Nijar sun yi maza sun yi lale marhabin da wannan sanarwa ta Macron wacce suka kwatanta a matsayin “sabon babin ‘yartar” da kasarsu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za su janye sojojinsu da jakadansu a Jamhuriyar Nijar saboda kifar da zababbiyar gwamnatin dimokradiyya da sojoji suka yi.

Macron ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi.

Sojojin na Nijar sun yi maza sun yi lale marhabin da wannan sanarwa ta Macron wacce suka kwatanta a matsayin “sabon babin ‘yartar” da kasarsu.

“Ba ma bukatar masu sabon salon mulkin mallaka a kasarmu.” Sojojin na Nijar suka fada cikin wata sanarwa.

Masu lura da al’amura sun kwatanta wannan al’amari a matsayin babban koma-baya ga manufofin Faransa a nahiyar Afirka.

Juyin mulkin da aka yi a Mali da Burkina Faso, ya tilasta ficewar dakarun na Faransa a ‘yan shekarun bayan nan a kasashen.

Ita dai Faransa ta jibge dakarunta a kasashen da ke yankin Sahel bayan da ta nemi iznin shugabannin yankin da zimmar yaki da ayyukan ta’addanci.

A Nijar, tana da dakaru 1,500, ta kuma ki kwashe su a kasar duk da sojojin juyin mulkin sun nemi su fice tare da jakadan kasar.

A ‘yan makonnin baya-bayan nan an yi ta kai ruwa rana tsakanin Faransa da Nijar wacce ta rena.

Macron ya ce jami’an diflomasiyyar Faransa na rayuwa bisa abincin da ake rabawa sojoji yayin da suke makale a ofishin jakadancin kasar.

Wannan sanarwa ta Macron na zuwa ne yayin da sojojin da suka yi juyin mulki suka sanar da shirin rufe sararin samaniyar kasar ga jiragen ‘yan kasuwa da na sojojin Faransa.

Wannan mataki bai shafi sauran jiragen saman kasa da kasa ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG