Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Fara Tattaunawa Da Jami'an Nijar Kan Janyewar Sojojinta – Jaridar Le Monde


Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron

Kasar Faransa ta fara tattaunawa da wasu jami’an sojin Nijar kan janye wasu sojojinta daga kasar da ke yammacin Afirka bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, in ji jaridar Le Monde a ranar Talata.

WASHINGTON, D.C. - A yanzu dai, ba a tantance adadin sojojin Faransa da ake shirin kwashewa ba, ko kuma lokacin da za su tashi don barin Nijar din, in ji jaridar ta Le Monde, inda ta ambato wasu majiyoyin Faransa da ba a san ko su wane ne ba.

Jaridar ta ce tattaunawar ba da shugabannin sojin juyin mulkin ake yi ba, amma da jami'an soji ne na yau da kullun waɗanda Faransa ta daɗe tana hadin kai da su.

Bayan juyin mulkin kasar Faransa wadda ita ta mulki kasar Nijar ta ce za ta kawo karshen hadin gwiwar soji da kuma yanke duk wani taimakon raya kasa da take baiwa Nijar.

Sai dai ya zuwa yanzu Paris ta yi watsi da kiran da shugabannin juyin mulki suka yi na janye sojojin Faransa 1,500 da ke Nijar a halin yanzu, tana mai cewa har yanzu tana kallon hambararren zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum, wanda a halin yanzu yake tsare a matsayin halartaccen Shugaban kasar.

Ma'aikatar tsaron Faransa ba ta ba da amsa kai tsaye kan bukatar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi mata ba.

Dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka taru a wajen wani sansanin sojin Faransa da ke Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar a ranar Asabar din da ta gabata inda suke neman sojojinsu su fice.

A cewar jaridar Le Monde, za a iya sake tura wasu sojojin Faransa daga Nijar zuwa wani yankin, musamman a makwabciyarta Chadi, yayin da wasu kuma za su iya komawa Faransa.

Sai dai janyewar kasar daga Nijar zai kasance wani cikas ga tasirin Faransa a yankin, bayan da ta fice daga Mali, inda sojojin haya na Rasha suka shiga.

Nijar ta kasance aminiyar Faransa da Amurka a fannin tsaro, wadanda suka yi amfani da ita a matsayin sansanin yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel na yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG