ABUJA, NIGERIA - Kungiyar ta kira taron ne na neman sasanci tare da hadin gwiwar kwamitin tsaro a matakin Ministocin kasashen inda suka jadada cewa hadin kai wajen dinke barakar shi ne mafita.
Wannan taron da ya zo kwanaki 11 cir bayan fitowar sanarwar kasashen uku ya tara ministocin kasashen ECOWAS da wasu masu ruwa da tsakin kungiyar ne a matsayin wani matakin neman a tattauna kan hanyoyin sasanci mafi sauki don gudun sanya al’ummar kasashensu cikin mummunar yanayi.
Dr. Omar Alieu Touray Shugaban Hukumar ECOWAS wanda ya bayyana cewa babu wani lokaci da ya dace mambobin kungiyar ECOWAS su hada kai kamar wannan lokacin kuma babu wani kalubalen dake gaban su da ba za a iya magance shi ba idan aka hada kai.
A yayin taron na yau dai, Ministan Harkokin Wajen Najeriya kuma Shugaban Majalisar Ministocin Kungiyar ECOWAS, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, ya jadada mahimmancin hadin kai wajen yin sasanci ga wannan barakar don gudun jefa al’ummar kasashen cikin mumunar yanayi.
Shi ma Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa za’a dauki matakan ‘yan uwantaka, mutunta juna da kare hakkin ‘yan kasashen nasu ta yadda zasu ci gaba da zama da juna cikin zaman lafiya da lumana.
A game da matsalar data kunno kai a kasar Senegal, Alhaji Badaru ya ce za’a bullo da matakan tabbatar da cewa an daidaita batun dage zaben kasar zuwa watan Disamba.
Idan ana iya tunawa, a cikin sanarwar da kasashen yammacin Afirka ukun wato Nijar, Burkina Faso da Mali suka fitar, sun jadada cewa zasu kare ‘yancin su a matsayin kasashe, kori kungiyoyin 'yan ta’adda, tare da nuna karara cewa shirya zabe ba shi ne babban abin da ke damun su ba a yanzu.
Tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ta yi ta kokarin ganin shugabannin sojojin kasashen sun dage wajen gudanar da zabe na maido da gwamnatin farar hula, lamarin da ya ci tura.
A ranar 28 ga watan Janairun da ya gabata ne kasashen na Mali, Nijar da Burkina Faso suka fitar da sanarwar ficewa daga kungiyar ECOWAS wanda zai fara nan take a cewarsu, lamarin da masana tsaro da siyasa suka ce matakin ya kawo karshen tattaunawar da ake yi na shirya zabe da kuma maido da mulkin farar hula a kasashen uku.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna