A wani taron wuni biyu da suka kammala, masana na Afrika ta yamma sun tattauna batun matsalar juyin mulki da soji ke yi a nahiyar musamman yankin yammaci, biyo bayan hambarar da gwamnatocin Burkina Faso, Mali, Guinea da kuma Nijar.
Tun 1975 mulkin dimokradiyya ke fuskantar koma baya a Afrika ta yamma, hankali ya tashi yanzu bayan sake kutsen da sojoji suka yi a wasu kasashen Africa.
A cikin shekaru ukun da suka gabata kasashen Afrika shida ne sojoji suka kifar da gwamnatocin dimokradiyya, abin da ya nuna samun koma baya ya kuma tada hankalin kungiyoyin masu fafutukar kare dimokraddiyya.
Alhaji Sani Gambo, masanin harkokin siyasa da tsaro ne a Nijar, yace nazarin su ya gano dalillan faruwar hakan, yana mai cewa hana doka ta yi aiki da kwadayin mulki na daga cikin abubuwan da ke haddasa juyin mulki.
Akwai kuma sauran dalilan da masanan suka bayyana, kamar talauci, rashin tsaro da kuma rashin aikin yi a tsakanin matasa. Masanan dai na ganin akwai bukatar a duba yadda shugabannin Afrika ke gudanar da mulki.
Shi ma a nasa bangare Traore Wedarago, wanda masanin harkokin yau da kullun ne a kasar Mali, ya nuna damuwa a kan katsalandan da sojoji ke yi a Afrika, yace dole ne a hanzarta duba matakan da suka dace
Ya kuma ce tsarin dimokradiyya na fuskantar kalubale mai yawa a Afrika, don haka akwai bukatar tuntubar juna a kan batun tsarin a tafi tare a gudanar da mulki wanda gwamnatocin yankin ya kamata su karfafa tsarin gudanar da zabe, tattaunawa ta shiga tsakani akan zaman lafiya, da mulki bisa kamanta adalci
Masanan sun bayyana cewa har yanzu wasu al’ummar Afrika na nuna sha’awa ga mulkin dimokradiyya duk da cewa mulkin ya gaza yi musu adalci
Saurari rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna