Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Shiga Nijar' Idan Har Aka Gaza Samun Sulhu - ECOWAS


Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)
Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta shirya shiga tsakani ta hanyar karfin soji a Nijar idan yunkurin diflomasiyya na kawo karshen juyin mulkin da aka yi a kasar ya ci tura, kamar yadda wani babban jami'i ya shaidawa manyan hafsoshin sojojin da ke taro a Ghana a ranar Alhamis.

WASHINGTON, D. C. - Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS Abdel-Fatau Musah ya zargi gwamnatin mulkin sojan da ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli da "wasan ja ni-in-ja ka" tare da kungiyar ta hanyar kin ganawa da wakilai da kuma neman hujjar kwace mulki.

"Sojoji da dakarun farar hula na yammacin Afirka sun shirya amsa kiran aiki," kamar yadda ya shaida wa manyan hafsoshin tsaro na kasashen kungiyar.

Ya lissafo ayyukan soji da ECOWAS ta yi a baya a Gambia da Laberiya da sauran wurare a matsayin misalan shirye-shiryen.

Ya ce "idan tura ta kai bango, za mu shiga Nijar ne da rundunoninmu da kayan aikin mu don tabbatar da mun maido da tsarin mulkin kasa, idan sauran abokan dimokuradiyya na son tallafa mana muna maraba da su."

Musah ya yi kakkausar suka kan sanarwar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bayar na cewa tana da abubuwan da za su gurfanar da Bazoum da ake tsare da shi a gaban kotu bisa laifin cin amanar kasa. Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai da ECOWAS duk sun nuna damuwarsu kan yanayin da yake ciki a tsare.

"Abin ban mamaki shi ne wanda ake tsare da shi ... kuma wai ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa, abin da ke ran kowa shi ne yaushe ya aikata laifin cin amanar kasa ke nan," in ji Musah.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG