Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ECOWAS Ta Shirya Wani Sabon Taro Kan Juyin Mulkin Nijar


Shugabannin ECOWAS
Shugabannin ECOWAS

A baya-bayan nan ne kungiyar ECOWAS ta yi taro a Abuja a cikin watan Agusta inda ta sanya wa'adin kwanaki 7 ga gwamnatin mulkin sojan Nijar don maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, ko kuma ta  fuskanci mummunan sakamako, wanda zai iya hadawa har da karfin soji.

To sai dai kuma gwamnatin mulkin sojan ta ki bin umarnin, maimakon haka ta zabi yanke alakar huldar diflomasiyya da Najeriya da sauran kasashen da ke goyon bayan dawo da Muhammad Bazoum kan karagar mulkin kasar.

Gwamnatin mulkin soja, a yanzu karkashin jagorancin kwamanda Janar Abdourahamane Tchiani, ta jajirce wajen yin tir da matsin lamba daga waje.

ECOWAS ta aike da wata babbar tawaga domin tattaunawa da shugabannin juyin mulkin tare da nufin shawo kan lamarin cikin lumana, amma tattaunawar ta hadu da cikas.

Tawagar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai murabus, ta hada da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar.

Tawwagar manzonnin kungiyar ECOWAS a karkashin shugabancin Janar Abdulsalam Abubakar da sarkin musulmi Sultan na Sokoto a Nijar
Tawwagar manzonnin kungiyar ECOWAS a karkashin shugabancin Janar Abdulsalam Abubakar da sarkin musulmi Sultan na Sokoto a Nijar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ke rike da mukamin shugaban kungiyar kasashen ECOWAS, ya bukaci a sake wani babban taron koli na musamman wanda ake sa ran zai wakana a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, 2023, a Abuja.

Taron zai tattauna ne kan yanayin siyasa da kuma abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar da kuma samo hanya mafi sauki don shawo kan lamarin.

A yayin taron, shugabannin ECOWAS za su zurfafa nazari kan yanayin siyasa mai sarkakiya da kuma yin shawarwari kan matakin da za su dauka.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta jaddada muhimmancin wannan tattaunawa dangane da abubuwan da ke faruwa a Nijar.

Yayin da lamarin ke kara ta'azzara, kasashen duniya za su ci gaba da sa ido domin ganin sakamakon wadannan muhimman shawarwari da matakai da kungiyar ECOWAS za ta dauka.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG