Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Hafsoshin ECOWAS Sun Fara Taron Wuni Biyu A Ghana


Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS Sun Fara Gudanar Da Taron Wuni Biyu A Ghana
Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS Sun Fara Gudanar Da Taron Wuni Biyu A Ghana

An soma gudanar da taron wuni biyu na manyan hafsoshin kungiyar ECOWAS a Accra babban birnin kasar Ghana a ranar Alhamis, a wani sashe na shirye-shiryen tunkarar juyin mulkin Nijar idan bukatar hakan ta taso.

ACCRA, GHANA - Taron wanda ya sami halartar manyan hafsoshin kungiyar kasashen ECOWAS tara, da suka hada da Najeriya, Ghana, Cote Diviore, Senegal, Togo, Benin, Liberia, Saliyo da kuma Gambia, zai maida hankali ne a kan batun yiwuwar aikewa da rundunar jiran ko ta kwana zuwa Nijar, idan ba'a sami nasarar shirin sulhu ba.

Taron na zuwa ne bayan da shugabannin kungiyar suka umurci rundunar sojin yankin da ta kasance a cikin shirin ko-ta-kwana a lokacin da suka gudanar da taro a birnin Abuja na Najeriya.

Yayin jawabinsa, ministan tsaron kasar Ghana Dominic Nitiwul mai masaukin baki, ya ce "ECOWAS na fama da matsalar rikici da muka san cewa ya kawo karashe shekaru da suka gabata da kasashe goma sha biyar na kungiyar suka zabi dora kasashensu a turbar demokardiyya."

Ya ci gaba da cewa "farin jinin ECOWAS ya daukaka ta fuskar duniya abin da ya sanya musu zuba jari karkata zuwa yammacin Afrika. Amma kuma a baya-bayannan, matsalar juye-juyen mulki ta fara ci mana tuwo a kwarya a yankin."

"Kasashen kudanci da gabashin Afrika suna zaman lafiya, yayin da muke ci gaba da baiwa kawunanmu matsala su, suna habbaka tattalin arzikinsu ta fanni samun masu zuba jari"

Ministan ya kuma jaddada matakin da Shugabannin kungiyar ECOWAS suka dauka yayin taronsu a birnin Abuja, inda yake cewa "Shugabannin kungiyar sun umurci rundunar sojin yankin ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin maido da kasar Nijar a turbar demokaradiyya, amma duk da haka kungiyar za ta ci gaba da tuntubar sojojin da suka hambarar da Gwamnatin farar hula a kasar ta Nijar ta hanyar diflomasiyya."

Ministan ya bayyana cewa yana da imanin hafsoshin sojin za su samar da dabarun da za'a yi amfani da su wajen amfani da karfin soja a jamhuriyar Nijar har in har bukatar hakan ta taso, tare da jaddada cewa har in masu tsaron Shugaban kasa a Nijar suna tsare da Shugabansu to ko shakka babu al’ummar yankin yammacin Afrika na cikin hatsari sosai.

Adib Sani, mai sharhi kan lamurran tsaro na ganin duk da matakan da ECOWAS ke dauka, ba za ta kaddamar da yaki a kan Nijar ba saboda mummunan tasirin da jibge dakarun ECOWAS a Nijar zai yi ma tsaro da tattalin arzikin yankin.

To sai dai wani batu da ya dau hankalin jama'a a gefen taron shine, ko ya kamata ECOWAS ta nemi izinin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya tukuna kafin ta dau matakin soji akan Nijar?

Dakta Abdul Fatau Musah, kwamishinan zaman lafiya da diflomasiyya na ECOWAS ya ce Majalisar Dinkin Duniya na da masaniya kan duk wani mataki da ECOWAS ta ke dauka kuma tana tare da ECOWA.

Kasashen Cape Verde da Guinea Bissau basu halarci taron ba bisa wasu dalilai, yayin da kuma babu wakilcin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da Guinea, saboda dakatar da su daga kungiyar kan matakan kifar da gwamnatocin farar hula da suka dauka.

Ana sa ran kammala taron a ranar Juma'a.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS Sun Fara Gudanar Da Taron Yini Biyu A Ghana.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG