Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Cutar Ebola ta Kashe Ya Karu


Ma'aikatan kiwon lafiya na ebola
Ma'aikatan kiwon lafiya na ebola

Sabon barkewar cutar ebola ya sa adadin wadanda suka mutu ya karu

Adadin wadanda cutar ebola ta kashe ya haura ainun daga dubu tara zuwa dubu tara da dari biyu.

Karin tamkar kira ne a farka daga barci idan aka yi la’akari cewa an yi makonni da dama ba’a samu sabbin kamu ba.

Alkaluman baya bayan nan da hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice ta fitar sun nuna cewa mutane 150 suka mutu kwana uku kacal bayan da hukumar ta sabunta rahotonta.

Hukumar tace an samu karin sabbin kamu 303 a kasashe uku. Liberiya ta samu sabbin kamu 136. Saliyo ta samu 113 kana Guinea ta samu 54.

Wakilin MDD na musamman akan cutar Ebola Dr. David Nabarro ya gayawa manema labarai a Geneva cewa kawo yanzu ba’a shawo kan wannan sabuwar barkewar cutar ba. Yace nufinsu ne a kawar da cuta kwata kwata.

A cikin wata wasika da shugabar Jamus Angela Merkel da Firayim Ministan Norway Erna Solber da shugaban kasar Ghana John Mahama suka rubutawa MDD sun ce barkewar cutar ya nuna raunin dake akwai akan yadda duniya take mai da martini idan an samu wani bala’i a duniya.

Sun mikawa babban sakataren MDD Ban Ki-Moon wasikar jiya Talata. Sun bashi shawarar ya kafa wani kwamiti mai iko wanda zai zana yadda duniya zata maida martani cikin gaggawa idan wani bala’i ya auku koina a duniya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG