Maganar faduwar darajar Naira na ci gaba da ciwa mutane tuwo a kwarya, wanda masana ke danganta wa da maganar dogaro da kayan da ake shiga kasar suna daya daga cikin abin da ke kawo wa Najeriyar koma baya kamar yadda masanin tattalin arziki Usha’u Aliyu ya bayyana.
Wani tsohon ministan man fetur a Najeriya Umaru Dembo cewa yayi an yiwa ‘yan Najeriya dodorido ne dama, don kuwa da ana samu ko da wutar lantarki ce da ‘yan Najeriya zasu iya taka rawar gani ta hanyar safarar kayan masarufi ta jirgin kasa da makamantansu.
Yace, idan Najeriya na da hikama ba zasu martaba maganar babban bankin bada lamumi na IMF ba indai har da gaske ne cewa kasar ta fi kowace kasa a nahiyar Afrika karfin tattalin arziki, duk da yake dai wasu suna cewa wannan abu da ake ta fada talaka bai sheda a kasa ba.
Ministan Kasa a Ma’aikatar kudin kasa Bashir Yuguda ya nuna cewa lallai Najeriya ita ce mafi karfin tattalin arziki, domin kuwa ta wuce takwararta wato Afrika ta kudu. Ya kara da cewa ta wuce sauran kasashen ne idan aka yi la’akari da yadda ba man fetur ne kadai man hajar Najeriya da ta ke cin kasuwarsu a duniya ba.