Shugaban ya bada wannan umurnin ne domin tabbatar wa ‘yan kasa cewa bashi da abinda zai boye daga yunkurin binciken da shugaba mai jiran gado, Janar Mohammadu Buhari yace zai yi dangane da gano yadda dala miliyan dubu ashirin din da tsohon shugaban babban bankin Najeriya, sarkin Kano Mohammadu Sanusi Lamido na biyu a yanzu yace sun salwanta daga kamfanin NNPC batare da an maido wa asusun gwamnatin Najeriya wadannnan makudan kudaden ba.
Wannan matsayin dai ya biyo bayan badakalar da aka yi ta yi dangane da kudaden da aka ce sun salwanta, wanda ya haura dala miliyan dubu arba’in da tara, amma daga baya kamfanin ya gano cewa kadan ne daga dala miliyan dubu biyu suka salwanta. Amma kuma akwai wasu hukumomi ko kamfanonin gwamnati, musamman bangaren man fetur da basu bada hadin kai wajen binciken ba.
Kakakin fadar gwamnatin Najeriya Dr. Rueben Abbati, ya fada wa manema labarai cewa shugaba Jonathan ba ya da abinda yake boyo saboda ya kwatanta adalci da gaskiya akan dukan al’amuran da yayi a lokacin da ya mulki Najeriya.
Mallam Gambo Hamza, kwararre a fannin tattalin arziki ya bayyana cewa binciken na da muhimmanci kammar yadda shugaba mai jiran gado ya kudurci zai yi saboda tamkar matashiya ce kamfani na price Water Coopers yayi domin a tabbabtar da gaskiyar abubuwan dake boye a rahoton.
An dai sha yin irin wannan binciken a baya amma kuma basu yi wani tasiri ba. Malam Gambo ya kara da cewa yana da tabbacin in har shugaba mai jiran gado ya hau kujerar mulki zai duba sakamakon bincike- binciken da aka yi a baya kuma zai dauki mataki.
Ga rahoton da Ummar Faruk Musa ya hada.