Ministan cikin gidan Nijar Malam Masud shi ya bayyana hakan ya kuma bada sakamakon artabun tsakanin sojojin kasar da 'yan Boko Haram.
A bangaren Nijar sojoji arba'in da shida suka kwanta dama kana tara suka jikata. Wasu talatin da biyu sun bace, ba'a san inda suke ba.
A bangaren 'yan Boko Haram dari da hamsin da shida aka kashe kuma fararen hula ashirin da takwas lamarin ya rutsa dasu har lahira.
Harin ya girgiza 'yan kasar ta Nijar. Sun nuna matukar juyayi tare da bada shawarwari ga gwamnati. Mutane sun yi ta'aziya ga iyalan wanda suka rasa 'yanuwa kana suka umurci gwamnatin kasar ta tanadawa sojojinta kayan aiki. Wajibi ne gwamnati ta dauki matakai kwarara domin irin harin na 'yan Boko Haram yana da tada hankali.
Ahalin yanzu gwamnati ta dauki matakai kwarara domin kare lafiyar jama'arta. Ta shiga neman sojojin da suka bace a lokacin artabun.Gwamnatin ta nuna alhininta ga duk iyalan wadanda suka rasa rayukansu da fatan wadanda suka jikata Allah ya warkar dasu. Gwamnatin tayi alakawarin samarda da kayan aiki domin kakkabe 'yan Boko Haram. Ta bayyana wasu 'yan kwanaki na zaman makoki a duk fadin kasar.
Ga rahoton Chaibu Mani.