Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kona Ofishin Jami'an Kiyaye Hadurran Hanya


Wuta
Wuta

An sami hatsaniya tsakanin matasan garin Kamfani a wajen garin argungu da ke jihar Kebbin Najeriya da jami'an hukumar kiyaye hadurran hanya ta kasa, wanda har yayi sanadiyyar jama'ar suka kona ofishin.

A yau ne jami’an kiyaye haduran hanya suka yi kokarin kama wani mai babur wanda hakan ya haifar da hatsarin da ya yi sanadiyyar rasa rauka har hudu a lokacin da suka tsaida mai babur din shi kuma ya kauce musu, sai wata babbar mota da ke bayansa ta kwace sakamakon rashin isashshen burki.

Kwacewarta ke da wuya sai da ta babbanke mutane har hudu suka kuma mutu nan take. Farruwar hakan ke da wuya sai matasan kauyen suka dunguma ofishin jami’an. Nan cacar baki ta sarke tsakaninsu da jama’ar da suka je ofishin bin ba’asi.

Matasan ba su tsaya wata wata ba sai kawai suka saka wa ofishin wuta suka kone shi. Konawar da ta yi asarar motoci da baburan hawan da su jami’an kiyaye hadurran ta kasa suka kama.

Kamar yadda wani shaidar gani da ido ya tabbatar a yayin da shima Kwamishinan ‘yan Sandan Kebbi ya Danladi Shabdiwala ya tabbatarwa da wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna faruwar lamarin.

Dama dai ana rade-radin cewa jama’a yankin na kule da su jami’an game da cewa suna takura musu a garin. Hukumar ‘yan sanda dai ta tabbatar da cewa zaya yi kokarin danko wadanda suka yi wannan ta’asa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG