Malam Bashir Ahmed magatakardan majalisar dokokin jihar Adamawa shi ya rantsar da Jerry Kundusi a matsayin sabon kakakin majalisar jihar.
Wani bangare na majalisar mai kunshe da wakilai guda tara daga cikin ashirin da biyar ya yi zamansa a gidan gwamnatin jihar a karkashin shugabancin 'yar majalisa Mrs. Wali Fua na wucin gadi. Ta gabatar da wata takarda mai dauke da sa hannun 'yanmajalisa 17 da suka amince a tsige kakakin majalisar Ahmed Umaru Fintiri.
Kafin a tsigeshi sai da ya yi zaman majalisar wadda ta dawo daga hutu. Bayan zama na wasu 'yan mintuna sai ya rufe. Zaman ya samu halartar 'yan majalisa 10 cikin su 25. Wasu shida sun gabatar da hujjojinsu na rashin halartar zaman.
To amma Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri yace har yanzu yana kan kujerarsa a matsayin kakakin majalisar. Ya zargi bangaren dake yiwa gwamna Ngilari biyayya da haddasa dambarwar siyasar da ta taso ta tsigeshi daga kan kujerarsa. Yace sun kulla makarkashiyar wawurar dukiyar jihar ne kafin su bar mulki. Yace majalisar daya ce kuma shi ne shugabanta. Amma wai sun samu labari cewa gwamnan jihar shi ya shirya tsigeshin.Yace sun yi zaman wawurar dukiyar gwamnati ne.
Shi ma Jerry Kundusi sabon kakakin ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana dalilan da suka sanya aka tsige Fintiri aka nadashi..Ya bada hujjoji uku. Na farko wai duk lokacin da aka kawo kudi majalisar a baiwa 'yan majalisar ba zai basu ba. Na biyu ya zabi wasu 'yan majalisa wadanda yake yin abubuwa tare dasu. Na uku wai yana cin fuskan 'yan majalisar tare da nuna rashin da'a ga gwamnan jihar..Ya hana 'yan majalisa su je su gaida gwamnan tunda Allah ya dorashi kan kujerar mulkin jihar.
Yanzu ba'a san wanda zai shugabanci majalisar ba idan ta sake zamanta.
Ga rahoton Sanusi Adamu.