Tun bayan da Majalisar Tarayyar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin kasar na bana ba tare da tanajin kason kudaden tallafin da akan bai wa masu shigo da tacaccen mai daga kasashen waje ba aka shiga cece-kuce. Hasali ma an yi watanni biyu babu man a wadace a sassan kasar, kuma ga shi kungiyar dillalan man fetur na barazanar shiga yajin aiki saboda bashin shigo da mai da ta ke bin gwamnatin kasar.
Wani tsohon Dan Majalisar Wakilan Najeriya kuma mai harkar dillancin man fetur mai suna Honorabul Alhassan Uba Idris ya gaya ma wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari cewa kin tanajin kudaden tallafin wata gadar zare ne gwamnatin PDP ke shiryawa ma Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari (murabus). Da wakilinmu ya tambaye shi ko idan babu tallafin ‘yan kasuwa ba za su iya shigo da mai cikin Najeriya ba, sai ya ce haka ne. Ya ce bashi yiwuwa ka sayo mai kan Naira 10 sannan kuma a ce sai ka sayar Naira 9 saboda ko uwar kudi ma ba ta dawo ba balle riba.
To saidai kuma Alhaji Babangida Lamido, masanin tattalin arziki kuma dan kasuwa a fannoni dabandaban na cinakayya ya ce tun daga Naira 65 aka cire kudin tallafi, saboda haka karawa aka yi ta yi kuma wasu ne ma ke karuwa da wannan karin. Ya ce an kago batun tallafin ne don kawai a karya matatun man Najeriya saboda wasu ‘yan gata su rinka fita da mai suna shigowa da shi, wani sa’in ma su shigo da marar kyau. Ya ce tunda Buhari ya ce zai farfado da matatun mai ya kuma gina wasu sabbi, wannan batun kudaden tallafin ma bai taso ba, dama an hana matatun man aiki ne. Don haka ya jaddada cewa cire tallafin man shi ne ya fi alheri ma kasar. Ya ce ‘yan boko ne kawai ke haddasa rudami a kasar saboda son kai, alhalin kuwa, za a iya sayar da mai a kasar akan Naira 60 muddun aka yi gaskiya.
Wakilin na mu, ya kuma tabo batun alkawarin da Buhari ya yi na binciken kudin kamfanin man Najeriya (NNPC) dala biliyan 20 da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma a yanzu Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya ce ya bace, wanda ke nuni da irin gagarumar gyarar da ke jiran bangaren man Najeriya.