Jiya Talata Najeriya ta bada labarin ta ceto kusan mata da ‘yan mata dari uku daga tungar ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, abunda ba’a tabbatar ba shine ko a cikin wadanda aka ceton akwai ‘yan matan ‘yan makaranta da ‘yan binidigar suka kama fiye da shekara daya yanzu dagagarin Chibok cikin jihar Barno. A cikin rahoto da wakilin Muyar Amurka Chris Stein ya aiko mana daga Legas yace masu magana da yawun rundunar sojin Najeriya sunyi bayanai masu karo da juna kan ko wadanda aka ceton ‘yan matan nan ne daga Chibok.
Rundunar sojin a shafinta na twitter ta bada sanarwar cewa ta ceto ‘yan mata metan, da mata 93 daga sansanonin ‘yan Boko Haram uku cikin dajin Sambisa, sai dai ba zata iya bada tabbacin cewa ko a cikinsu akwai ‘yan matan nan da aka sato daga Chibok ba.
An hakikance cewa dajin Sambisa shine tunga ta karshe da ‘yan binidigar suke da ita a arewa maso gabashin kasar. A farkon wannan watan ne sojojin kasar suka bada labarin zasu kai farmaki cikin dajin a wani bangare na kamfen da suke yi na gamawa da ‘yan binidigar masu tsatstsauran ra’ayin Islama.
Kakakin rundunar kasar Manjo Janar Chris Olukolade yace sojojin suna ci gaba da yaki da nufin kama dajin baki dayansa.
Yace ana ci gaba da tafiyar da wannan mataki, domin mun kakkabe sansanoni da muka tantance zamansu. Akwai wasu sansanoni da muka gano a bayanan ayyukan leken asiri wadanda tilas ne suma mu wargaza su.
Pogo Bitrus shine shugaban kwamitin dattijan Chibok kuma wakili ne na iyalan ‘yan matan da aka sace a Chibok. Yace daya daga cikin iyalan da yayi magana dashi yana nuna kwarin guiwa kan labarin da aka samu.
Yace Idan muka tantance cewa wasu daga cikinsu ‘yan matan Chibok ne, to zamu fara murna”.
Iyalan suna da hujjar nuna shakku. Domin a baya an bada bayanai kan sakin ‘yan matan wadanda basu tabbata ba. Jim kadan bayan an sace ‘yan matan , sojoji suka yi kuskuren cewa an ceto galibin ‘yan matan. Cikin watan Satumban bara rundunar ta sake bada wani rahoton cewa an gano wasu ‘yan matan amma bayan ‘yan sa’o’I suka lashe aman d a suka yi.
A birnin New York, jakadan Majalisar Dinikin Duniya na musamman kan harkokin ilmi, Gordon Brown, yace labarin an ceto ‘yan mata metan, koda daga ina ya fito labari ne dayake faranta rai.
Ga karin bayani.