Guguwar dake mataki na 4 da sauka ta banya kasa ne da tsakar dare, inda ta haddasa barna mai yawa a yankunan bakin teku ta hanyar kifar da kananan jiragen ruwa da kada bishiyoyi da jawo makalewar motoci da malalewar tituna da ruwa, kamar yadda hotunan da aka samu daga garuruwan Tampa da Naples da St. Petersburg dake gabar ruwan Florida suka nuna.
A cewar gwamna Ron Desantis na jihar Florida wanda ya tabbatar da mutuwar wani direba da karikitai suka afkawa motarsa, “idan muka wayi gari gobe da safe, akwai yiyuwar samun karin wadanda zasu mutu.”
Kamfanonin rarraba hasken lantarki sun bayyana cewar, fiye da mutane miliyan 1 da 200 a Florida da 800, 000 a Georgia suka yi fama da daukewar wutar lantarki.
Cibiyar nazarin guguwa ta Amurka (NHC) ta bayyana cewar, a jumlance Helene ce guguwa ta 14 mafi karfi a tarihin Amurka, kuma ta 7 mafi muni da aka gani a Florida.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna