Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya 130 Daga Sudan Sun Sauka A Abuja


'Yan Najeriyar da aka dawo da su gida saboda barkewar rikicin Sudan (Hoto: Facebook/NIDCOM)
'Yan Najeriyar da aka dawo da su gida saboda barkewar rikicin Sudan (Hoto: Facebook/NIDCOM)

Hukumar NIDCOM da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce da misalin karfe 3:15 na yamma jirgin kamfanin Tarco mai lamba B737-300 ya sauka a Abuja.

Wani rukunin ‘yan Najeriya da ya taso daga Port Sudan ya sauka a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Juma’a.

Wannan rukuni na biyu mai dauke da mutum 130, mata 128 maza biyu, ya sauka ne a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Hukumar NIDCOM da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce da misalin karfe 3:15 na yamma jirgin kamfanin Tarco mai lamba B737-300 ya sauka dauke da mutanen.

Tun bayan da rikici ya barke a Sudan, ‘yan Najeriya mafi akasari dalibai suka yi ta ficewa daga kasar. Kasashen duniya da dama ma ciki har da Amurka sun kwashe jama’arsu.

Masu tserewa rikicin da dama sun nufi kasar Masar domin neman mafaka ko kuma gwamnatocinsu su kwashe su.

A farkon makon nan Najeriya ta cimma matsaya da Masar kan yadda Najeriyar za ta kwashe ‘yan kasar ta cikin kasar ta Masar.

Gabanin hakan, sama da mutum dubu abkwai sun yi dafifi a kan iyakar Sudan da Masar ciki har da ‘yan Najeriya, bayan da Masar ta hana mutane shiga ba tare da takardun biza ba.

Wannan rukunin ‘yan Najeriya da ya sauka a ranar Juma’a shi ne na biyu a jigilar da hukumomin Najeriya ke yi na jama’arta wadanda ke tserewa yakin Sudan.

XS
SM
MD
LG